Gazwul Fikriy 01
Gazwul Fikriy 01 A farko-farkon 'karni na Ashirin ne, Mustashrikun suka fahimci yakar al'ummar Musulmi da makami da karfin soja babu abinda yake haifarwa face karin tsana da tirjiya daga matasan Musulmai akamsu, abinda ba zai haifar musu d'a me ido ba, saboda haka sai suka yi tunanin wata hanya ta daban ta yakar Musulmai, wacce ba zata gadar da kiyayya da gabarsu a zukatan matasanmu ba. Saboda haka sai suka yi tunani akan Gazwul Fikriy (yakar tunani da kwakwalwa), ko da yake irin wannan yaki ya jima a tsawon tarihi, amma dai ba'a taba ganin zamanin da yakin yake ci kamar wutar jeji kwatankwacin irin wannan zamanin ba. Ta hanyar wannan yakin ne Makiya suka kyankyashe mana Almaniyyawa daga cikinmu, masu magana da yarenmu, masu sanya irin tufafinmu tare da cin irin abincin da muke ci, amma kuma babu abinda suka tsana a duniya sama da Addinin mu da shari'armu da kyawawan al'adunmu na Islama. Irin wannan yaki yana da manufofi da hanyoyin hakkak...