Gazwul Fikriy 01

Gazwul Fikriy 01

A farko-farkon 'karni na Ashirin ne, Mustashrikun
suka fahimci yakar al'ummar Musulmi da makami
da karfin soja babu abinda yake haifarwa face karin
tsana da tirjiya daga matasan Musulmai akamsu,
abinda ba zai haifar musu d'a me ido ba, saboda
haka sai suka yi tunanin wata hanya ta daban ta
yakar Musulmai, wacce ba zata gadar da kiyayya da
gabarsu a zukatan matasanmu ba.
Saboda haka sai suka yi tunani akan Gazwul Fikriy
(yakar tunani da kwakwalwa), ko da yake irin
wannan yaki ya jima a tsawon tarihi, amma dai ba'a
taba ganin zamanin da yakin yake ci kamar wutar
jeji kwatankwacin irin wannan zamanin ba.
Ta hanyar wannan yakin ne Makiya suka kyankyashe
mana Almaniyyawa daga cikinmu, masu magana da
yarenmu, masu sanya irin tufafinmu tare da cin irin
abincin da muke ci, amma kuma babu abinda suka
tsana a duniya sama da Addinin mu da shari'armu
da kyawawan al'adunmu na Islama.
Irin wannan yaki yana da manufofi da hanyoyin
hakkakashi, daga cikinsu:
1) Keta tushen Musulunci da turakunsa, kamar
jefama mutane shakku acikin al-Qurani da Sunna da
Tarihin Musulunci gyarararre da Tuhumar Sahabbai
da tuhumce-tuhumce, da yada sabaninsu abin
yafewa.
2) Gurbata Aqidun Musulunci da shari'arsa da
alamominsa ko gurabensa.
3) Yakar yaren Larabci me cike da azanci.
4) Kokarin rarraba kan al'umma kungiya da kungiya,
jama'a jama'a.
5) Dulmiya al'umma cikin wasanni da sha'awa.
Zamu yi nazari akansu a hankali..

Comments

Popular posts from this blog

YAR. HUTU

*«»«»«»SAIFUDEEN!«»«»«»*

_DACEWA_