_DACEWA_
*_DACEWA_*
_(when east meets west)_
_By_
_Mamuh geee_
*_Viawattpad@mamuhgee_*
*50-51*
Gudu take sosai tana kallon gefensa dayake kallonta da idanuwansa dake qoqarin rufewa yana murmushi jini na zubowa daga bakinsa.
Hannuta 'daya ta miqa ahankali ta kama nasa tana hawaye murya na rawa tace,
I love too Ahmed,, ina sonka har cikin raina so mai tsanani so am begging you not to leave me pls Ahmed., ina sonka...
Saukar harbi taji cikin motar tasu ta 'dago da sauri taga motarsu zeey ce taredasu leloh ta figi motar ta qara gudu.
Harbin motarsu suke tako ina inda ayeesha ta fixge bindigar hannun leloh ta saita kan neesah tana cewa lets finish this today.
Harbowa tayi Ahmed ya yunquro da 'dan qaramin kuzarinsa ya tare bullet din ya sauka a tsakiyar bayansa.
Wani wahalallen nishi yasaki tareda zubewa jikinta.
Sakin motar tayi tareda rungumosa tana rintse ido tace,
Let's die together my Ahmed.
Daji motar tafara gangarawa dasu Wanda hakan yafara Jan hankalin motocin dake wucewa suka fara tsayawa da sauri su leloh suka tsaya daga nesa dan kar agane su suka biyosu.
Wani qaton rami motar ke qoqarin fa'dawa bayan tafara kamawa da wuta Ahmed ya tattaro wani qarfi ya tura 6an6areta jikinsa tareda turata waje da qarfi ta window riqe hannunsa tayi tana ihu tana kiran sunansa ya kalleta a wahalce yace,
Neeees'''bai qarasaba sulbin Jinin hannuwansu yasa ta sulbuce daga hannusa ta ganngara gefe kanta ya daki wani qaton dutsi nan take ta sume motar ta fa'da tareda kamawa da wuta sosai.
Ajiyar zuciya suka sauke kusan duk atare ganin yanda wuta kecin motar sun tabbatarda bamai Rayuwa tsakanin neesah da Ahmed.
Kallon zeey ayeesha tayi cikin samun wani cikakken kwanciyar hankali tace,
Finally I got all I ever wanted.
Cikin taya aminiyarta farin ciki tace,
Well then lets all wish you a happy married life wit your captain,,you alone.
Juya kan motarsu sukayi suka bar gurin hankalinsu a kwance.
Aliyu mamman aliyu shine babban aminin Ahmed yana kawowa gurin yaga daidai lokacinda motar ke qoqarin fa'dawa rami yakuma tabbatarda motar neesah ce ya fito motarsa da sauri amma kafin ya iso motar ta fa'da tareda kamawa da wuta amma yaga lokacin da neesah ta gangaro ta daki dutsi.
Gurinta ya qarasa da sauri ya 'daukota yana kallo motar ta cinye tas da wuta ga amininsa aciki duk da kuka yake sosai kamar qaramin yaro.
Motar police ce tareda tasa suka 'dauko gawar Ahmed daya qone qurmus bayan an kashe wutar tareda neesah dake sume kamar gawa suka nufo cikin gari.
Asibiti suka fara kai neesah tareda barin 'yan sanda biyu gadinta kafin suka nufi gudansu Ahmed da gawarsa Wanda isarsu yayi daidai da isowar dady daga tafiyarsa.
Koda aka ciro gawar gaban dady aka bu'de saura qiris ya zube saida aliyu yayi saurin tarosa daidai fitowar Jamaal sbd jiniyar dayaji tashigo har cikin harabar gidan.
Gabansane yayi mummunar sarawa yayi saurin dafa motar sbd mahaukacin jirin daya 'dibesa.
Xubewa yayi gaban gawar tareda dafe kansa hawaye suka gangaro daga idanuwansa a karo na farko arayuwarsa tun tashinsa baita6a koda hawaye ba bare kuka sai yau dayaga gawar Ahmed.
Rawa jikinsa keyi sosai kamar qaramin yaro ko mgn yakasayi.
Khadija ce tashigo harabar gidan cikin motar ta tun kafin tai parking jikinta yayi masifar sanyi ganin kamar gawa gabansu dady tanayin parking ko key bata tsaya cirewaba ta fito da sauri jikinta na rawa.
Cak ta tsaya gaban gawar tareda qurawa gawar ido tagano tabbas Ahmed ne duk da ya qone sosai amma ta gane shine hannu ta 'dora akai tareda sakin kuka mai qarfi ta zube a qasa.
Inna Rabi ce ta fito da hanxari jin ihun khadija
Itama wani qaqqaran salati tasaki tareda fashewa da kuka ahankali.
Duk da tana cikin tsananin damuwarda ko motsi bata son yi sbd azabar ciwon kai dake damunta haka ta miqe jin hayaniya harabar gidan gashi inna Rabi data leqa bata dawoba.
Turus ta tsaya ganin gawa ga khadija daketa kiran sunan ahmed 'din tana kuka kamar ranta zai fita.
Jiri me qarfine ya 'dibeta tayi baya Jamaal ya dago tsalle ya tareta ta rintse idanu saiga hawaye sun 6alle masu qarfi sbd sobon son Ahmed 'dinta da wani mugun tausayinsa da kewarsa dasuka rufeta lokaci 'daya ta fashe da kuka ahankali mai shiga rai tana tunanosa.
Duk iya tashin hankali iyalan gidan sun shiga dan kowa kuka yake sosai sbd Ahmed 'din abin son kowane.
Har aka shiryasa aka rufesa aka dawo bamai iya magana sbd sosai mutuwarsa ta ta6a kowa na gidan musamman ummi data zabge lokaci 'daya ga wani irin ciwo da zuciyarta keyi.
Har washe garin rasuwarsa neesah bata farfadoba sbd likitoci sun tabbatarda sosai ta bugu akai.
Mamynta datazo ita ke jinyarta sbd inna Rabi ayyuka sun mata yawa na mutane dan gidan kusan acike yake sosai da mutane.
Sai ranar daza'ayi adduar uku ta farfado tana ihu tana kiran sunan Ahmed kamar zararra.
Daqyar aka samu ta saurara sbd allurar da akai mata ta kashe jiki.
Lamo tayi jikin mamy hawaye nabin fuskarta amma tanajin ra'da'di da zafi a zuciyarta amma ko juya idonta bazata iyayiba bare ta motsa sbd allurar da akai mata.
Duk iya yanda aka tsammata daga gareta alamarin ya wuce nan dan sosai
Zabure zabure takeyi duk lokacin da allurar tasaketa harsai ankuma yimata wata.
Cikin kwana 'daya tashin hankalinsu ya ninku bayan na rasuwar Ahmed sbd sabon alamarin dake tattareda neesah,
Kallo 'daya zakai mata tabaka matuqar tausayi sbd yanda ta yamutse ta rame kamar wadda tayi jinyar shekaru gashi kowane lokaci yanxu cikin bacci take sbd allura da ake mata koda yaushe sai hakan ya ta6ata matuqa dan wani irin haske da yellow yellow tayi kamar mai wani ciwon.
Kuka mamy keyi sosai sbd tsaf tarigada tagama hango ta6in hankali atattare da neesah ga rashin abinci da ciwo dake cin qwaqwalwarta sun sauyata sosai.
Doctors biyar ne suka taru suka duba result 'din hoton qwaqwalwarta suna jinjina alamarin.
Babban Consultant 'din cikinsu shiya 'dago ya kalli Abba da dady sai Jamaal dake gefensu tsaye shima duk ya rame yayi wani 'dan haske yace,
Well alhaji I'm really sorry to say this but a iya qwarewar bincikenmu mun gano buguwar da kanta yayi tareda mummunan firgitar rasa wani ko tsoron wani yasa qwaqwalwartata yanxu bazata iya aiki daidaiba saidai nan zuwa da 'dan wani time idan komai yafara ragewa daga firgicin datake cikin by god grace muna sakaran everything will fall to its normal place saidai yanxu kada a ringa matsa takurata sosai da tambaya ko kuma wani Abu dazai firgitata.
Ajiyar zuciya suka sauke atare Abba yayi masa godia suka miqe suka fito office 'din jiki ba qwari.
Tunda Jamaal yadawo gida ya kwanta a kujerar palonsa yakejin nauyin qirji Sam ko bu'de idanuwansa baya sonyi sbd Jan dasukai tun ranar da komai yafaru har rasuwar Ahmed dakuma ciwon neesah yakejin kamar zuciyarsa zata buga sbd komai ya qara shige masa duhu babban abinda yafi 'daure musu kai shine harbin bullet biyu dasuka gani ajikin Ahmed 'duk daya qone amma saida 'yan sanda suka gano kuma sun 'dauki hotunan guraren domin gudanar da bincike amma yanxu neesah da itace only hope 'dinsu itama tasamu ta6in qwaqwalwa.
Ayeesha ce da tun washe garin ranar rasuwar tadawo tana kukan munafurci Wanda ko kallo bata ishi ummi ma sbd ganin take duk cikinta ne sanadin komai har Ahmed 'dinta ya rasa ransa
Fitowa tayi daga bedroom ta zauna kusadashi tareda 'dan kwantawa jikinsa tace,
My us navy captain pls kayi hkr ka rage damuwarnan sbd tanasani damuwa nima kawai tunda sun Riga sun tafi sai mu haqura koba komai Ai haqqin kashe mana baby ne yafita a kan....
Idanuwansa daya bu'de ne suka masifar razanata ta miqe tareda ja baya da sauri.
Batareda yace komaiba ya maida idanuwansa ya rufe sbd ko kallonta baya buqatar yaci gaba dayi dan zai iya yi mata komai akan zancenta daya daki zuciyarsa.
Khadija ma sannu ahankali ciwon zuciyarta ya kwantar da ita sbd damuwar rasuwar Ahmed data shigeta sosai ga wani irin tausayin kanta dana neesah dake shigarta akowace daqiqa.
Ummi ma dai sauqi sai agurin Allah sbd Sam takasa daina kukan rasuwar Ahmed saima wata sabuwar soyayyar neesah dake shigarta sbd saiyanxu tagane sona haqiqa Ahmed yayiwa neesah dan haka yanxu kamar amanar Ahmed take ganin neesah.
Ummi da kanta ta daure a daddafe ta shirya zata asibiti dubo neesah.
Shigowar ayeesha tayi daidai da fitowarsu ummi da mamar khadija dake gidan tun bayan rasuwar bata komaba.
Khadija ce tafito itama duk ta qarmaje ta zabga uwar rama sbd ciwo sake cinta.
Gaidasu ayeesha tayi tareda qaqalo murmushi tace,
ummi fita zakuyune keda bakyajin da'di.?
A 'dage mama ta kalleta sbd Sam ta tsani matar Jamaal dan ita 'yarta khadija taso 'daya daga cikin 'yayan ummi su aura amma ko yanxu ba sakin kari tayiba saita tattara wannan tsinanniyar ayeeshar ayeeshar ta watsar waje khadijarta tasamu damar zama matar Jamaal suyi ku'di kamar yanda take buri.
Mama hatsabibiyar mace ce dazata iya tarwatsa gida cikin awa 'daya komai taronsu da ha'din Kansu.,babban burinta khadija ta auri Jamaal ko Ahmed sbd dukiyarsu da sunansu batareda tasan itama khadijar Jamaal take kwa'daitawa kanta tuntuni.
Tsaf mama ta tsani ayeesha kuma da manufar fiddata gidan kota halin qaqa yasata fasa komawa tacewa yayanta( _dadynsu Jamaal_) anan zatayi zamanta dan dama batada aure sbd babansu khadija da qanwarta maryaam ya da'de da rasuwa.
Murmushin qeta tasaki tareda kallon ayeeshar tace,
Asibiti zamuje dubo kishiyarki aneesah.
Jiri ne yakusa zubar da ita ta dafa kujera jikinta na rawa cikin tashin hankalin daya kasa 6oyuwa tace,
Neesah bata mutuba ne?
Ummi mama ta 'dan kalla sbd ganin tambayar ta ayeesha ta 6ata mata rai saita saki mugun murmushi tace,
Bangane wannan tambayar takiba da kinason ace ta mutu ne?
Yawu ta ha'de tafara kame kame
mama tasaki murmushi tabi tawuce sbd sarai taga takaicin maganar ayeeshan a idon ummi.
Suna ficewa Palon ta zube qasa zuciyarta na tafasa akan jin labarin rashin mutuwar neesah gefe 'daya taga alamar idan tayi wasa mama zatafisu iya tsula iskanci.
Da gudu takoma part 'dinsu ko gani batayi ta rarumo wayarta takira zeey ta fada mata.
Wani wawan ashar zeey ta sako tareda dirowa daga gadon datake kwance cikin masifa tace,
Dole a daran yau basai gobe va muje asibiti mu qarasata sbd idan tadawo hankalinta mungama yawo.
Mamuh💋
🌲 *R H F W F*🐄
_Don't forget to vote, follow and comments_
Comments
Post a Comment