*«»«»«»SAIFUDEEN!«»«»«»*

*«»«»«»SAIFUDEEN!«»«»«»*

          By
  *Billy giro😊*

*Dedicated to»»»Zarah gwandu*

*«»page«» 52*

Saif dake shafa bayanta muryar sa  a hankali yace"jikin ki yayi zafi sosai zarah,meyasa kikayi tayin kuka har zazza6i ya kama ki haka plz indai akan wnn mtr ne ki cire damuwa a ranki komai zai daidaita kinji"
  Zarah dake manne a jikin sa a hankli ta gyad'a masa kai,yace"kinci abinci?
Ta girgiza masa kai,ya kalli abincin da aka ajiye mata nn kusa da gefen gado cikin plate an rufe da d'ayan plate fresh milk da cup ajiye a kusa yace"bari to na d'auko maki abincin kici"
Muryar ta can qasa ta marasa lfy tace"um um bana iya ci bakina baya min dad'i,kawai cire min wnn qarin ruwan da ake min ni na gaji dashi.
Tayi maganar ne had'e da miqa masa hannun ta da aka d'aura mata ruwa akai.
Saif ya kama hannun nata a hankali zai cire mata,se ganin sukayi an tizge mata cannula d'in da qarfin tsiya har sai da jini ya fito aguje ba shiri,zarah ta fasa ihu cike da jin zafi wacce kafin ta iya ganin wanda ya tizge mata cannula d'in se jin tayi an kuma fizge ta daga jikin saif had'e da kai mata lafiyayyen mari har sai da ta fad'i kanta ya daki beside drawer,ta fasa ihu tare da dafe gefen kan ta,a rikice saif yaje da sauri ya kamata tuni gefen kanta ya fashe jini na fita nn saif ya d'ago idanun sa da duk sukayi jajur lokaci d'aya,cikin tsananin 6acin rai yake kallon mom d'in sa da duk ita ce tayi aikin,sosai ya jimqe hannun sa jikin sa na wani irin rawa yana jin kmr yaje ya doke ta amma be iya yin hakan ba se qwalla da suka taru a idon shi,ya kalli zarah da sai kuka take zai tafi da ita jikin sa dmn ya rarrashe ta,ta tafi da gudu jikin Umman kd da shigowar ta knn d'akin ita da Nadiya kan jin ihun zarah da yasa su zowa da sauri sbd duk basu san da shigowar mom d'in saif ba dmn saif na barin falon bayan ta kira Abban kd a waya ita ma ta tashi ta nufi kitchen a niyyar zata kawo musu lemu a can Nadiya ta same ta dan koda ta sauka bata ga kowa a falon ba,bcos umman kd na barin falon jamil ya tashi ya fita yaje cikin mota ya zauna sbd kansa dake masa masifar ciwo ya had'e kan nasa da sitarin mota shiyasa har mom d'in saif ta shiga cikin gida baiga wucewar ta ba.
Ae kuwa da mamaki umman kd ke kallon mom d'in saif snn ranta a 6ace tace"masifaffiya masifar taki kuma kika zo zakiyi ta a nn ko kuma kinzo zaki kashe tan ne iye! ta kama hannun zarah ta kai mata ita tace"gata ki kashe ta in san cewa ke cikakkiyar  marar hankali ce me lasisi.
Mom d'in saif dake kallon ta tace"Kome zaki kirani indai akan d'ana ne ni bazan damu ba,amma ina son in gaya miki idan har na sake ganin ta a karo na uku tare da d'ana sai dai ku nemi wata er wlh babu kuma abunda zaku iya yi,idan kuma kinyi gardama mu zuba nida ku shege ka fasa.
Daga haka ta fita daga d'akin duk ranta a 6ace ta wuce Abban kd da isowar sa knn qofar d'akin zai shiga ya bita da kallo kana ya qarasa daga ciki yana kallon su umma yace"lafiya me kuma ya kawo ta a gidan nn"
  "D'anta ta biyo mana"
Umman kd ta bashi amsa tare da kama hannun zarah dake ta kuka suka fita daga d'akin har Nadiya.
  Abban kd ya bisu da kallo kana ya juya gun saif yayi tsaye yana kallon saif da ya zauna kan bed tare da dafe kanshi irin cikin damuwa d'in nn,nn ya qarasa kusa dashi ya zauna ya dafa shi a hankali,saif ya d'ago idanun sa da suke jajur kuma cike tap da qwallah muryar sa na rawa sbd 6acin rai da kukan da yake ji yace"Abba ni kam wace irin uwa ce wnn na had'u da ita dan Allah kasa a d'aure ta dmn wlh na fahimci ba hankali ne da ita ba zata iya kashe zarah da gaske.
Abban kd yace"tabbas kuwa amma kaine kasa hankalin nata ya gushe,kuma kaine zaka iya dawo mata da hankalin nata.
  Da kamar mamaki Saif yace"kmr ya Abba na bita kake nufi ko kuma na rabu da zarah wanne kake nufi ciki?
Abban kd yace"ae dama ita zarah kun rabu....da sauri yace no Abba zarah she is still my wife wlh a bisa kuskure na rubuta mata saki kuma....is ok basai ka sake maimaita min bayani ba naji komai na kuma fahimci iya inda kake da laifi,but still zarah baza ta koma maka ba sbd a cikin bayanin da aka min da akwai inda na fahimci lallai ba son zarah kakeyi ba wata qil shaquwar zaman da kukayi ne yasa duk kabi ka damu da rabuwar auren ko kuma ince jin ita wace ce a gun umman ka yasa duk kaji idan kuka rabu baka kyauta ba shiyasa kake son a mayarda auren ko?
A sanyaye saif yace"ba haka bane Abba"
  To yaya ne?
Ina son cikawa Abba burin sa ne.
Ya fad'a cikin marairaicewa.
Abban kd yace"ka gaya min gaskiya rasuwar sa ce tasa kake son cika masa burin sa ko tun kafin ya rasu ne kake son ganin ka cika masa burin nasa?
Saif yace"eh tun kafin ya rasu"
Abba dake kallon sa yace"meyasa zaka min qarya saif bayan kafin na tambaye ka sai da nace ka gaya min gaskiya"
  Saif yace"Abba gaskiya na gaya maka wlh"
Abba ya girgiza kansa yace"wnn rayuwar da ka d'aukowa kanka sam bata dace da kai ba saif,idan har gaskiya ka gaya min meyasa to har Abban naka ya rasu ba abunda ya ta6a shiga tsakanin ka da zarah.
Da sauri saif ya kalli Abban kd se kuma ya sadda kansa qasa yayi shiru bai ce masa komai ba.
Abban kd yace"ko kuma ba haka bane da akwai?
  A hankli saif ya girgiza kansa yace"babu"
Abban kd yayi shiru  yana kallon sa can ya jinjina kansa yace"hm saifuddeen knn a hkn ne to kake da burin samarwa Abban ka farin cikin sa har kana fad'in zaka maida auren ka da zarah bayan kulata ma baka iyayi,but shikenan dai yanzu abunda nake so dakai daga yau ka d'auke qafar ka da zowa gurin zarah dmn babu zancen maida auren ka da ita,kabar jamil dake sonta yaci gaba da zowa gurin ta har Allah yasa su sasanta tsakanin su suyi aure.
A rikice saifudeen ya kalli Abba da yaji zancen nasa kmr saukar guduma,muryar sa na rawa yace"Abba meyasa,dan Allah kayi haquri zaman da mukayi a baya sam ba irin shi zamuyi ba yanzu wlh cike nake da burin samarwa Abba farin cikin sa.
  Abban kd yace"na gama fahimtar ka saifuddeen dan haka ka daina cutuwar kanka kana fad'ar abunda fad'a kawai kake ko an barka baza ka iya aikatawa ba,abunda kawai nake so dakai shine ko kad'an kada kayi wasa da yiwa Abbanka addu'a dmn abunda yafi buqata knn a gurin ka yanzu.
Mahaifiyar ka kuma ina son kayi haquri ka cire komai a ranka ka mata biyaya dmn sam ban gaya maka halinta dan ka tsane ta ba sai dan ina tsoron kar wata manufa ce yasa tazo zata tafi dakai shiyasa na gaya maka dmn koda ta tafi da kai d'in zaka iya kare kanka daga sharrin ta,amma a yanda na fahimce ta bada nufin cutuwa ta dawo gare ka ba qauna ce,wacce idan ba binta kayi ba hankalinta bazai ta6a kwanciya ba haka muma da kai karan kanka,dan haka kawai kayi haquri ka bita duk lokacinda ka buqaci ganin mu kai namiji ne zaka iya zowa ka kawo mana ziyara akoyaushe amma idan zakayi aure kasan irin macen da zaka aura kar kayi irin kuskuren da Abban ka yayi da farko,da kuskuren ne yazo yana ta bamu matsala a yanzu,Allah de ya kyauta.
   Saifudeen dake jin kuka da qyar ya iya had'iye kukan yace"Abba ni gaskiya bazan iya bin wnn matar ba,burin ta fa taga cewa ta rabani da ku kwata kwata.
Abba yace"ka ta6a ganin inda aka raba mutum da iyayen shi ae wnn sai dai mutuwa"
  Yace"to ba gashi ba Abba se biye mata kukeyi har kuna cewa zarah baza ta koma min ba"
  Cikin d'aure fuska Abba ya kalle sa yace"we are all educated dan haka kar ka sake yunqurin maida mu shashashai,abunda kawai nake son ji shine gaya min ita mahaifiyar taka a ina take nufin ka bita a can gidan ta na kano da naji ance ta kaika ka ko kuwa Maiduguri?
Saif dake jin wani qololon baqin ciki ya danne abun yace"Nima ban sani ba kawai dai tace min ko kano d'in nake son inci gaba da zama zata yarda amma kune bata so inci gaba da kulawa wai.
Abba yace"fad'a kawai take ita kanta tasan bazata ta6a iya rabamu dakai ba,haukar son ganin ka koma gare ta ne kawai ke d'ibar ta,dan haka ka daina tunanin wae zata iya raba mu dakai mutuwa ce kad'ai ta isa tayi hakan,snn ko barin ka da zamuyi ka koma gurin ta dan ita mahaifiyar ka ce da ta haifeka hkn yasa zamu barka ba dan masifar ta ko wani abu ba ka fahimce ni?
  Saif da duk haushi yake ji a ransa ya gyad'a masa kai kawai.
Nan Abban kd ya tashi ya fita daga d'akin,saif da ya bisa da kallo shima ya tashi ya fita duk ransa a 6ace ya tafi sai d'akin umman kd,se ganin Abban kd yayi a can yaje duba zarah da har an mata dressing kan inda taji ciwo haka ma hannunta a samu jinin ya tsaya.
Suna had'a ido da Abban kd ya sadda kansa qasa fuskar nn tasa ba annuri yana gudun kar Abban kd d'in yace mai me yazo yi gun zarah kuma,Abban kd kuwa shi a tunanin sa ma ko yazo yiwa umman kd sallama ne zasu wuce,wanda har ya nufi qofa ze fita se kuma ya tsaya yace da saif kafin ku wuce kace da jamil yazo ina son zamuyi magana nida shi.
  Bansan taya ma zan misalta muku abunda saif yaji ba dan ko magana ma kasa yiwa Abban kd yayi,wanda yana gama fad'a ya fita ba tare da ya jira me saif d'in zai ce ba.
  Nan umman kd da Nadiya suma suka fita daga d'akin sbd sun fahimci saif da zarah yake son zai yi magana,wacce tana ganin sun fita ta tashi da sauri itama zata fita,saif ya rigata isa bakin qofar d'akin yasa key ya rufe snn ya kama hannun ta a fusace ya tafi da ita ya manna ta a jikin bango yana kallon ta idanun sa jajur cike da qwallah with deep voice yace"ke wace irin yarinya ce mai fallasa sirrin aure da har zaki bi mutane duk ki gaya musu cewa wai ba abunda ya ta6a shiga tsakani na dake gashi duk kinsa Abba se ganin laifi ne yake akan hakan!
Zarah da duk ta kame guri d'aya qwallah tap a idonta muryar ta na rawar kuka tace"to ba kai bane ka gaya ma umma"
  A hankli saif ya sassauta riqon da ya mata yana tuna hakane fa se kuma lokaci d'aya ya sake manna ta a jikin bangon yace"ta yaya akayi to suka san cewa har bayan rasuwar Abba ba abunda ya had'a ni da ke idan bake kika gaya musu ba!?
  Tace"to ae duk laifinka ne tun farko,da baka gaya ma umma ba da baza ma su nemi jin qarin bayani daga gare ni ba.....ke kuma wawiya shine se kika gaya musu bayan duk kece kika hana faruwar komai,to wlh bari kiji in gaya miki yanzun nn zan nunawa Abba cewa u are still my wife babu wani d'an iskan da ya isa ya aure ki nine mijinki na har abadah wlh.
  Nan kawai ya hau zare belt d'in wandon sa,a tsorace ta saki  kuka ta kame jikinta sosai tana bashi haquri dmn a tunanin ta ko dukan ta zai yi amma se ganin tayi ya jefar da belt d'in ya kuma zuge zip d'in wandon shi nn ta fahimci abunda yake niyya ai kuwa da sauri ta bud'e ido had'e da girgiza masa kai.
Bai kula ta ba sai jefa ta yayi kan bed ya haye ruwan cikinta tare da had'e bakin sa da nata dan kar tamai ihu su Abba suji bai samu yayi abunda yayi niyya ba,wanda yana had'e bakinsa da nata yakai hannun sa zai raba ta da doguwar rigar da ke jikinta,zarah bata iya zare bakinta ba se kokawa ta shiga yi dashi a hakan duk yabi ya yaga mata riga,snn ya koma kan undies d'inta suma ze yaga,nn ta samu da qyar ta zare bakinta daga nashi cikin kuka ta shiga bashi haquri tana fad'in ya daina kar ya aikata nn fa d'akin umma ne,amma fir yaqi saurararta ganin haka yasa kawai ta shiga yin ihu tana kiran umma.
  Koda su umma suka ji ihun ta suka zo a rikice sai dukan qofar suke baza su iya bud'ewa ba sbd key d'in da saif yasa,dolen su suka zagaya ta d'akin Abban kd da akwai qofa a can da zasu iya shiga d'akin,sukayi sa'a kuwa qofar a bud'e take saif gabad'aya ya manta da qofar bai rufe ba.
  Sai jin yayi sun shigo d'akin,Abban kd ya nufo shi a fusace ya 6an6anre shi daga jikin zarah tare dakai masa lafiyayyen mari yace"d'an iska me kakeyi haka get out ! in daina ganin ka a nn very stupid!!
Idanun saif ne suka ciko tap da qwallah ya tsaya se huci yake yana kallon zarah da tuni umma ta kamata tasa bedsheet ta rufe mata jikinta,zarah ta rungume ta sosai sai kuka take tana kallon saif ya juya kawai ya fita daga d'akin,a ransa yana fad'in lallai yau kome zata zama sai dai ta zama shi Hjy zai je ya sama idan itama taqi goya mai baya to kuwa sai dai dashi har zarah a neme su a rasa dan kuwa wlh zai d'auke ta ne ya tafi da ita inda ba wanda ya sani bare ace za'a rabashi da ita.

Jamil da still yana nn cikin mota kansa had'e da sitari,duk abunda yake faruwa shi bai ma sani ba haka sam baiji shigowar saif cikin motar ba se jin yayi an rufe ganbun motar da qarfi,ya d'ago kansa da qyar ya kalli saif muryar sa a hankli yace"lafiya ka shigo mota haka ina zarah ba tare zamu koma bane?
  Saif da duk haushin jamil yake ji cikin tsawa yace"da Allah malam ni kaja mota mu bar garin nn!
  jamil ya kalle sa kawai baice masa komai ba ya lalla6a yaja motar suka hau hanyar komawa kano.
Da shigar su garin kano ne wayar saif dake laqe tana caji ta shiga ringing wacce ya neme ta ne yau da safe shine ya ganta a under pillow.
Ya kalli wayar tashi ransa a mugun 6ace kmr bazai d'aga ba amma ganin Nusaiba ce me kiran yasa ya d'aga kiran.
  Yana d'aga kiran nata yaji sai kuka take sosai tana fad'in"Dan Allah yaya kayi sauri kazo tun d'azun se kiran numbar su Abban kd nake ban samu ba mom d'inka ce tazo da police sun tafi da umma.
Da sauri saif yace what! a wane police station ne tasa aka je da ita?
Tace"nima ban sani ba amma ka fara zuwa gidan ta tukun dan bata bisu ba sawa kawai tayi suka wuce da umma wae idan baka bi umarnin ta ba baza ta sa a fidda umma ba.
  Nan kawai ya tsinke kiran ya kalli jamil da ke tambayar sa lafiya wa aka rufe? Yace"bani motar inja dawo nn 6angaren yau sai na nuna mata na fita hauka wlh!.
Cikin rashin fahimtar abunda yake faruwa jamil yayi kmr yanda saif yace,saif yaja motar a tsiyace inda Allah ne kad'ai yasa suka isa gidan mom d'in tashi lafiya.
  Ya faka motar a bakin gate ya shiga cikin gidan kmr wani zautacce se bud'e duk room d'in da ya gani yake yana neman inda zaiga mom d'in tashi har Allah yakai shi room d'in qarshe da gefen room d'in ya zama kamar wani part na daban kan yanda akayi doguwar hanya ya tafi can daban da sauran d'akuna.
  Yana bud'e d'akin yaga yanayin d'akin kmr clinic room har ma da patient kwance akan bed an sanya masa oxygen amma baya ganin fuskar patien d'in sosai sbd mom d'in sa dake tsaye a gaban patient d'in riqe da allura a hannunta zata yiwa patient d'in,wacce jin an bud'e qofar yasa ta juyo da sauri tana ganin saif ne a tsorace ta saki allurar,nn gaban saif yayi wani irin mugun fad'uwa ya tsaya cak cikin tsananin tashin hankali da tsoro ya bud'e ido yana kallon fuskar Abban sa da shine patient d'in.

Comments

Popular posts from this blog

YAR. HUTU

_DACEWA_