Buhari ya hana shugabannin APC yin tazarce.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci
Babban Kwamitin Zartarwar (NEC) jam'iyya mai
mulki ta APC da kada ya sabunta wa'adin
shugabannin jam'iyyar.
Lokacin babban taron jam'iyyar a watan jiya ne aka
amince da aka kara wa shugabanni wa'adin shekara
guda.
Sai dai wadansu daga cikin jagororin jam'iyyar ciki
har Mista Bola Ahmad Tunubu sun nuna adawarsu
ga hakan.
A jawabin da ya gabatar yayin babban taron
jam'iyyar wanda aka yi jiya Litinin, Shugaba Buhari
ya umarci dakatar da tsawaita wa'adin shugabannin
saboda kaucewa ce-ce-ku-ce kuma yin hakan ya
saba wa kudin tsarin jam'iyyar, a cewarsa.
Sai dai yayin da yake ganawa da manema labarai
bayan taron,mai magana da yawun jam'iyyar Malam
Bolaji Abdullahi ya ce an kafa wani sabon kwamiti
wanda zai duba wannan batun.
Har ila yau ya ce ana saran kwamitin zai mika
shawarwarinsa akalla zuwa gobe Laraba.
Jam'iyyar APC dai na fama da rikicin cikin gida,
musamman a rassan jam'iyyar da ke jihohin kasar.
Kuma wadansu na ganin matakin da shugaban ya
dauka ba zai rasa nasaba da karatowar zabukan
shekarar 2019 ba.

Comments
Post a Comment